Adawar siyasa ta fara daidaita a Kano — Gwamna Abba

Gwamnan ya ce addu’ar da aka yi za ta kawo mafita game da rikicin Masarautar jihar.

Adawar siyasa ta fara daidaita a Kano — Gwamna Abba

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce adawa da dangantakar siyasa a jihar na ƙara inganta, kuma yana da yaƙinin cewa za a samu mafita game da rikicin Masarautar Jihar.

Gwamnan ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnati na aiki don ganin an warware matsalar ta hanyar da kowa zai ji daɗi.

Ya bayyana hakan ne yayin taron addu’a ta musamman da karatun Alƙur’ani da aka gudanar a gidan Gwamnatin jihar.

Mahaddata 4,444 ne suka halarci taron domin yi wa jihar addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai da cigaba.

A cewar sanarwar da mai magana da yawunsa ya fitar, gwamnan ya ce addu’o’in sun fara samar da sakamako mai kyau, inda ya ce an fara samun fahimtar juna a tsakanin abokan hamayya na siyasa.

Ya kuma ambaci halartar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, wasu tarukan gwamnati a matsayin haɗin kan siyasa.

Gwamna Abba, ya ce yana fatan addu’o’in za su taimaka wajen samar da mafita game da rikicin Masarautar jihar.

Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙarin haɗa kan ’yan siyasa, tare da roƙonsu su guji siyasar “a mutu ko a yi rai” face su rungumi mutunta juna domin ci gaban Kano.

Haka kuma ya jaddada aniyar gwamnatinsa na yaƙi da faɗan daba, yana mai cewa matasan da ke yin daba da su daina tare da mayar da hankali wajen bayar da gudunmawa ga al’umma.

Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan da za su inganta rayuwar jama’a.

A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yaba da taron addu’ar aka gudanar, inda ya ce sauran jihohi su koyi da Kano.

Tun da farko, Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya buƙaci al’umma su ci gaba da addu’a domin ci gaban Kano da Najeriya baki ɗaya.