An sa ranar fara kwaso alhazan Najeriya daga Saudiyya

Za a fara kwaso alhazan Najeriya daga Saudiyya a ranar 22 ga watan na Yuni, 2024.

An sa ranar fara kwaso alhazan Najeriya daga Saudiyya

A ranar Litinin 10 watan Yuni, 2024 sahun karshe na maniyyatan jihohin Najeriya za su tashi zuwa Kasa Mai Tsarki.

Hakan na zuwa ne a yayin d Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta sanar cewa za a fara kwaso alhazan Najeriya daga Saudiyya a ranar 22 ga watan na Yuni, 2024.

Maniyyata 211 da suka rage daga jihohin Bauchi, Kebbi, Neja, Sakkwato, Zamfara da kuma Abuja za su tashi a jirgin karshen daga Abuja zuwa Madina ne a yayin da ya rage kwana uku a fara aikin Hajjin shekarar 1445 Hijiriyya.

Jirgin na kamfanin FlyNas shi ne kuma zai kwashe rukunin karshe na jami’an aikin Hajji kamar yadda Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta tsara.

Da haka NAHCON za ta kammala kwashe maniyyatan jihohi yadda ta tsara, duk da tsaiko da ka samu a sakamakon yajin aikin da ƙungiyoyin kwadago suka gudanar a makon da ya gabata.

A ranar Litinin din dai kamfanin Aero contractors zai kammala jigilar maniyyatansa na jirgin yawo daga Najeriya.

Sauran kamfanonin jiragen yawon kuma ana sa ran za su kammala kwashe maniyyatansy daga Najeriya kafin a rufe filin jirgin sama na biranen Madinah da Jeddah.

’Yan bindiga sun sace Farfesa, sun nemi N10m kuɗin fansa

Za a ɗauke wutar lantarki na tsawon mako 2 a Abuja

Hukumar tace fina-finai ta dakatar da Samha kan shigar banza

Sakataren Gwamnatin Ondo ya rasu bayan yin hatsarin mota