Yau Kotun Ƙoli ke sauraron shari’ar Jam’iyyar ADC da DPP

A yau Litinin Kotun Koli za ta yi zama kan shari’o’in da ke gabanta kan rikicin shuganci da ya dabaibaye jam’iyyun adawa na ADC da PDP.

Yau Kotun Ƙoli ke sauraron shari’ar Jam’iyyar ADC da DPP

A yau Litinin Kotun Koli za ta yi zama kan shari’o’in da ke gabanta kan rikicin shuganci da ya dabaibaye jam’iyyun adawa na ADC da PDP.

Zaman kotun zai gudana ne a ranar da jam’iyyar ADC take gudanar da babban taronta na kasa, inda ake sa ran tabbatar da sabbin shugabanninta.

Wannan na zuwa ne bayan umarnin kotu na mayar da abubuwa yadda suke a baya a jam’iyyar, bayan karar da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, Nafiu Bala Gombe ya shigar yana kalubantan sabon shugabancin jam’iyyar karkashin jagorancin David Mark.

Duk da ƙalubalen da ke neman yi mata tarnaƙi gabanin zaɓen shekarar 2027, Jam’iyyar adawa ta ADC ta ce ta kammala shirya tsaf domin gudanar da Babban Taronta na Ƙasa a yau Litinin.

ADC, jam’iyyar da ke ƙara farin jini a Najeriya ta shiga tsaka mai wuya ne bayan ƙarar da ɓangaren tsohon mataimakin shugabanta na ƙasa, Nafiu Bala Gombe, ya shigar yana ƙalubalantar halaccin shugabancin Mark.

A nata bangaren, Jam’iyyar PDP tana fama da rikicin shugabanci tsakanin bangaren tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Kabiru Tanimu Turaki da kuma tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.