Yawan mamata a harin jirgin soji a kasuwar Zamfara ya haura 150 —Shaidu
Wani mazaunin garin ya yi zargin yiwuwar ’yan bindiga sun samu bayani daga masu yi musu leƙen asiri
Shaidu sun bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu ya haura 150, wasu sama da 40 kuma na karɓar magani a asibiti bayan harin da jirgin sojin Najeriya ya kai a Kasuwar Tufa da ke Jihar Zamfara.
Wani dattijo mai suna Malam Abdullahi Hassan, ya shaida wa wakilinmu cewa ba a jima ba barinsa kasuwar da dabbobin da ya saya, jirgin yaƙin ya kai harin.
Malam Abdullahi ya ce, “Muna zaune muna hira da tsofaffi irina, sai na kawai sai na fara jin fargaba, ba ni da natsuwa, har suka tambaye ni me ke damu na? Sai na ce musu, halin da muke ciki yana damu na sosai, yadda muka koma kamar bayin ’yan bindiga. Daga nan hirar tamu ya watse.
“Bayan na koma gida ina duba dabbobin da na sayi, sai na ji wani ƙara mai karfi sosai, shi ne muka yi sauri zuwa wurin. Gaskiya babu wanda zai iya faɗin ainihin yawan mutanen da suka mutu, saboda wasunsu sun zama toka, amma mun waɗanda ba su lalace ba, sun kai mutum 150, in ji Malam Abdullahi.
- NAJERIYA A YAU: Halin da matan da aka yi garkuwa da suke ciki
- ’Yan sanda sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane a Katsina
Shi ma wani mazaunin yankin, wanda ya rasa danginsa mutum biyar a harin, amma ya nemi kada a bayyana sunansa, ya bayyana cewa, ’yarsa da ƙaninsa sun samu munanan raunuka daga harin. Ya bayyana cewa bayan ya baro kasuwar ne jirgin sojan ya kai harin.
“Ina shirin yin alwalar Sallar Azahar sai na ji ƙarar bom ɗin. Nan take muka wuce zuwa kasuwar, ƙanina ɗan auta, duk jikinsa jina-jina, ’yata kuma kusan karaya biyu ta samu.”
Ya bayyana cewa kafin harin, ɗaruruwan ’yan bindiga a kan babura sun shigo yankin, amma kafin jirgin ya kawo harin sun riga sun bar garin. Ya yi zargin yiwuwar an tsegunta musu ne suka tsere kafin a kawo harin.
A cewarsa, “’Yan bindigar da na gani a kasuwar za su kai mutum. Ina ƙofar gida sukazo suka wuce a kan baburansu, amma ba mu sani ba, ko an kira su a waya ne aka gaya.”
Ya bayyana cewa waɗanda aka kashe, yawancinsu ƙananan yara ne masu sayar da abinci da kayan maƙulashen gargajiya.
“Ina cikin waɗanda muka yi aikin binne mutanen. A cikin amalanke muka riƙa kwatsam gawarwakin zuwa maƙabarta, tsawon awa tara. Gawarwakin sun farfashe kamar tsummokara.”
A cewarsa, babu ko ɗan bindiga ɗaya da aka kashe a harin an ranar Lahadi, kuma babu wata musayar wuta da aka yi tsakanin sojoji da ’yan bindiga kamar yadda rundunar soji ta yi iƙirari.
“Ni dai ban ga gawar wani ɗan ta’adda, tun da mun san su, ba za su yi mana wuyar ganewa ba, mun gane duk waɗanda aka yi wa jana’iza,” in ji shi.
“’A kan ’yanmu masu tallar furta da awara bom ɗin ya faɗo, kuma a lokaci guda mun binne mutum 80, daga baya aka gano wasu gawarwaki da tarkacen bom ɗin ya danne da kuma wasu a cikin baraguzan ƙasa.”
Ya bayyana cewa ana da mutum 40 da suka jikkata a harin suna karɓar magani a Asibitin Gusau.
Amma ya jaddada cewa, “Gaskiya babu faɗan da aka yi tsakanin sojoji da ’yan ta’adda. Hari ne dai jirgi ya kawo inda ya jefa bom a kan ’ya’yanmu da ’yan uwansu da ke harkokin kasuwancinsu a Kasuwar Tufa.
Shi ma wani mazaunin garin ya yi zargin yiwuwar ’yan bindiga sun samu bayani daga masu yi musu leƙen asiri, game da yiwuwar harin, shi ya sa suka bar yankin.
Ya ƙara da cewa yawan mamatan ya kai 150, da yiwuwar samun ƙarin saboda har yanzu akwai waɗanda ba a gani ba.
“Ina neman yayana a cikin gawarwakin sai wasu sojoji suka zo wurik suka yi ta harbe-harbe a iska, suka kwashe baburan da ’yan bindigar da sauran kayan jama’a da suka bari.