Za a samu ambaliya da ruwa mai karfi a jihohi 15 a Arewa —NEMA
Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen hasashen ruwan sama mai karfi da ka iya haifar da ambaliya a Jihohi 15 a yankin Arewacin Najeriya
Ambaliya a Afirka ta Kudu
Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen ruwan sama mai karfi da zai iya haifar da ambaliya a jihohi 15 na Arewacin Najeriya da wasu wurare 68, a cikin kwanaki biyar masu zuwa.
Wannan gargadi ya fito ne daga Cibiyar Lura da Gargadin Ambaliya ta Kasa, karkashin Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, inda aka bukaci hukumomi da al’umma su dauki matakan gaggawa don kare rayuka da dukiyoyi.
Cibiyar ta bayyana jerin jihohi da wuraren da ambaliyar za ta iya shafa sun hada da:
- Adamawa: Jimeta, Mubi, Mayo-Belwa, Wuro-Bokki, Yola, Farkumo
- Bauchi: Jama’a
- Nasarawa: Keffi
- Kaduna: Jaji, Kafanchan, Zaria, Birnin-Gwari
- Katsina: Katsina, Bindawa, Kaita
- Kebbi: Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega, Bunza, Birnin Kebbi, Bagudo, Argungu
- Kano: Bebeji, Gwarzo, Karaye, Sumaila, Tundun-wada
- Niger: Rijau, Ibi, Chanchaga, Magama, Mashegu, Minna, Mokwa, New-Bussa, Sarkin Pawa, Wushishi
- Taraba: Duchi
- Jigawa: Miga, Ringim, Hadejia, Dutse
- Yobe: Potiskum, Dapchi, Gasma, Gashua, Jakusko
- Zamfara: Kaura Namoda, Maradun, Shinkafi, Bungudu, Gusau
- Sokoto: Sokoto, Gagawa, Gada, Goronyo, Isa, Wamakko, Silame, Makira
- Borno: Bama
- Kwara: Jebba
Hukumar Kula da Halin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta bayyana cewa kawo yanzu mutane 140,228 a jihohi 21 ne ambaliya ta riga ta shafa a shekarar 2025.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Damina Ke Shafar Masu Ƙananan Sana’o’i
- Ambaliya: Mutum 165 sun mutu a Nijeriya a bana — NEMA
Hukumar Kula da Halin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta bayyana cewa kawo yanzu mutane 140,228 a jihohi 21 ne ambaliya ta riga ta shafa a shekarar 2025.
Alkaluman da NEMA ta fitar sun nuna ceaw ambaliyar ta riga ta raba mutane 49,205 da muhallansu, ta lalata gidaje 10,663, da kuma gonaki 9,454 a al’ummomi daban-daban.
Jihohin da ibtila’in ya fi shafa sun hada da:
Imo (28,030), Ribas (22,345), Adamwa (12,613), Abia (11,907), Delta 8,810, Borno (8,164), Kaduna (7,334), Bayelsa (5,868) da Legas (5,793).
Sauran jihohin sun hada da Akwa Ibom (5,409), Niger (3,786), Ondo (3,735), Edo (3,234), Kogi (2,825), Sokoto (1,916), Kwara (2,663), Kano (1,446), Jigawa (1,428), Gombe (972), Anambra (925), da Babban Birnin Tarayya (1,025).
Da haka hukumar ta bukaci jama’a da hukumomi da su dauki matakan gaggawa don rage illar ambaliya da kare lafiyar jama’a.