Sauya sheka: Muna tattaunawa da Kwankwaso da Obi — Bala Mohamed
Bala Mohammed ya ce, zai koma wata jam’iyyar da ta fi karko domin shiga zaben da ke tafe
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce ya fara tuntubar wasu jam’iyyun siyasa, kuma zai sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar PDP nan da mako guda.
Gwamnan yana shirin barin PDP ne sakamakon rikicin cikin gida da ya kai ga soke taron gangamin jam’iyyar da aka yi a Ibadan.
Da yake tabbbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa da wasu manyan ’yan adawa, Bala Mohammed ya ce, “Muna tattaunawa da Rabiu Kwankwaso da Peter Obi.
“Ana kira ga ’yan adawa su hade a karkashin dandalin guda, amma ba abu mai sauki ba ne. Yanayin siyasa ya bambanta daga jiha zuwa jiha da kuma bukatun jama’a,” in ji gwamnan.
- Talauci da Rashin Tsaro: Tinubu ya ayyana dokar ta-baci
- Kwankwaso zai sauya sheƙa daga ADC zuwa Jami’yyar NDC
- Rikici ya barke a Jam’iyyar APC kan takarar zaben 2027
A baya, tawagar Jam’iyyar ADC karkashin jagorancin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ta ziyarce shi ga Gidan Gwamnatin Bauchi bisa umarnin shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata David Mark, domin shawo kansa ya koma ADC.
Bayan ganawar, Gwamna Bala Mohammed ya bayyana ADC a matsayin jam’iyyar da zai fi so ya koma idan har ya bar PDP.
Daga bisani, gwamnan ya yi wata ganawa da Shugaban Kasa Bola Tinubu da wasu manyan jagororin APC. Bayan nan, Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, ma ya jagorance shi a Bauchi domin lallashinsa.
Sai dai tattaunawar ta rushe saboda rashin jituwa kan yadda za a raba ikon jam’iyyar da sauran tsare-tsare. Shugaban bangaren PDP na jihar karkashin jagorancin Tanimu Turaki, Samila Adamu Burga, ya zargi APC da kin amincewa da tsarin siyasar gwamnan.
A hirarsa da BBC Hausa, bayan kotun koli ta soke taron gangamin PDP na Ibadan, Gwamna Bala Mohammed ya ce sun karbi hukuncin kotu da hannu biyu.
Ya bayyana cewa zai koma wata jam’iyyar da ta fi karko domin shiga zaben da ke tafe. “Duk da taronmu na Ibadan an soke shi, nasu shugabanci ma an rushe. A halin yanzu, kwamitin amintattu zai rike jagoranci har sai an kafa shugabanci na wucin gadi,” in ji shi.
Gwamnan ya zargi Ministan Abuja, Nyesom Wike, da rura wutar rikicin PDP, yana mai cewa matakan da ya dauka sun raunana jam’iyyar daga cikin gida.
“Mun tsinci kanmu cikin mawuyacin hali. Wike da abokanansa da dama suna tare da APC. Zamansa a PDP domin tarwatsa jam’iyyar ne, kuma hakan ya yi tasiri. Amma duk da haka mun tabbatar bai samu cikakken iko ba.
“Saboda karancin lokaci, mun fara tuntubar wasu jam’iyyu domin ’yanmu su samu damar tsayawa takara,” in ji Mohammed.
Ya kara da cewa akwai shirin samar da dan takara guda daya na shugaban kasa a kasar. “An yi hakan ne da gangan domin su shiga zabe ba tare da kalubale ba. Duk da biyayyarmu ga PDP, ba mu da wani zaɓi sai mu duba wani dandalin siyasa.
“A cikin ’yan kwanaki, za mu kammala tattaunawa kan inda za mu koma. Shugabannin PDP karkashin Tanimu Turaki za su ci gaba da bin lamari, mu kuma za mu ba wa magoya bayanmu damar tsayawa takara a wasu jam’iyyu. Nan da mako guda, za mu bayyana matsayarmu a Bauchi,” in ji shi.
Ya roki magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, yana mai tabbatar da cewa ’yan takara za su samu damar shiga zaben da ke tafe.
Dangane da burinsa na siyasa, gwamnan ya ce ba zai tsaya takarar shugaban kasa ba, domin jam’iyyar ta ba da takarar ga yankin Kudu.
Amma ya bayyana cewa zai tsaya takarar kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu. “Ba zan tsaya takarar shugaban kasa ba. Mun amince a matakin jam’iyya cewa kujerar ta koma Kudu don adalci. Amma bisa kira daga jama’ata, zan tsaya takarar Sanatan Bauchi ta Kudu domin ci gaba da wakiltarsu da kuma tallafawa,” in ji shi