Zulum zai mayar da ’yan gudun hijira 5,000 Bama

Gwamnan ya ce suna da ci gaba wa ‘yan gudun hijira matsuguni domin su koma gidajensu.

Zulum zai mayar da ’yan gudun hijira 5,000 Bama

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa na shirin mayar da mutum 5,000 gida daga sansanin ‘yan gudun hijira kafin wucewar damina domin su samu damar yin noma.

Mutanen za su fito ne daga garuruwan Goniri, Bula Kuriye, Mayanti, Abbaram, da Darajamal.

Gwamnan, ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai wa Mai Martaba Shehun Bama, Dakta Umar ibn Kyari Umar El-Kanemi, ziyara a fadarsa da ke Bama.

Ya ce an riga an kammala gina matsuguni 1,000 a Darajamal, sannan kuma aikin gina wasu a sauran garuruwan hudu.

“Mun ƙudiri aniyar dawo da ‘yan gudun hijira gida. A Mayanti, Goniri, Bula Kuriye da Abbaram muna gina gidaje, na Darajamal kuma an riga an gama,” in ji Gwamnan.

Ya ƙara da cewa gwamnati za ta kewaye yankunan da rami domin inganta tsaro.

Zulum, ya jaddada muhimmancin noma a rayuwar al’umma.

“Muna so mutanen da za a dawo da su gida su samu damar yin noma, saboda noma shi ne abin dogaron rayuwa a Borno,” in ji shi.

Ya ce zai gana da shugabannin JTF da Civilian JTF domin tsara yadda za a kare lafiyar manoma da gonaki.

Haka kuma, Zulum ya shaida wa Shehun Bama cewa gwamnatinsa ta ƙara tsaurara tsaro a garin Nguro Soye, domin samun damar yin noma.

“Daga dawowa daga Gwoza, na tsaya a sansanin sojoji da ke kusa da Banki, inda muka tattauna yadda za a tsaurara tsaro a Nguro Soye. Na bai wa sojoji da Civilian JTF kayan aiki kuma na yi alƙawarin biyan ‘yan sa-kai da ke sintiri alawus ɗin watanni shida da suka wuce,” in ji Gwamnan.

A nasa ɓangaren, Mai Martaba Shehun Bama ya yaba wa Zulum bisa ƙoƙarinsa na kyautata tsaro da jin daɗin jama’a.

“Ina yi wa gwamna godiya saboda dawo da mutanen Darajamal gida. Muna fatan sauran mutane ma za su dawo gida cikin kwanciyar hankali,” in ji Shehun.

Shehun, ya kuma roƙi gwamnatin da ta ƙara tallafa wa Civilian JTF domin kare manoma da gonaki a lokacin damina.