Abin Al’ajabi ya janye daga neman takarar Majalisar Tarayya 

A wasiƙar da ya aike wa Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kaduna, Honorabul Mahmud Sadis Buba, ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon ƙoƙarin sasanta rikice-rikicen cikin gida da shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka fara.

Abin Al’ajabi ya janye daga neman takarar Majalisar Tarayya 

Matashin nan da labarin fitowarsa neman takarar Majalisar Tarayya ya karaɗe kafofin watsa labarai, Honarabul Mahmud Sadis Buba, wanda aka fi sani da Abin Al’ajabi ya janye aniyarsa.

Ƙafin janyewar, da farko Mahmud Sadis ya fito neman takarar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Sabon Gari a Jihar Kaduna a ƙarƙashin Jam’iyyar APC.

Amma a cikin wasiƙar janyewarsa da ya aike wa Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kaduna, Honorabul Mahmud Sadis Buba, ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon ƙoƙarin sasanta rikice-rikicen cikin gida da shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka fara.

Hakan kuma, yana zuwa ne a yayin da ke ci gaba da ce-ce-ku-ce game da yawan shekarunsa, inda wasu rahotanni ke nuni da cewa an haife shi ne a watan Agustan shekarar 2010.

Hakan na nufin shekarunsa 16 kuma sun gaza mafi ƙarancin yawan shekarun da doka ta ƙayyade ga duk mai neman tsayawa kujerar majalisa a Najeriya.

Labarin Abin Al’ajabi ya karaɗe kafofin watsa labarai ne bayan ɓullar bidiyonsa a lokacin da ya mayar da fom ɗinsa na neman takarar kujerar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Sabon Gari a ofishin APC.

A yayin tantancewar ya bayyana cewa al’ummar mazaɓarsa ne suka buƙaci ya fito takarar kujerar, kuma ya amsa kiran.

Mai tambayar ta nemi sanin shekarunsa, inda ya bayyana cewa ya haura shekara 25.

Ya kuma shaida mata cewa ya kammala karatun sakandare, har ya gabatar da sakamakon jarabawarsa ta Hukumar Shirya Jarrabawa ta Ƙasa (NECO).

Daga bisani an yi ta yada hotunan matashin tare da shugabannin siyasa na APC, kamar Shugaba Bola Tinubu da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani.