Gobarar Singa: Tinubu ya jajanta wa ’yan kasuwar Kano
Shugaban ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano musababbin tashin gobarar.
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya jajanta wa ’yan kasuwar Kano, waɗanda suka tafka asara sakamakon mummunar gobarar da ta tashi a kasuwar Singa da ke Jihar.
Tinubu, ya bayyana lamarin a matsayin abun tausayi tare da umartar a gudanar da cikakken bincike kan musabbabin tashin gobarar.
- El-Rufai ya aike wa Ribadu takarda kan zargin shigo da guba mai hatsari cikin Najeriya
- HOTUNA: Har yanzu gobara na ci gaba da ci a Kasuwar Singa da ke Kano
A cikin wata sanarwa ta bakin mai bainwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya ce ya tuntuɓi gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, domin samun rahoton halin da ake ciki game da gobarar.
Idan ba a manta ba AminiyaAminiya ta ruwaito yadda gobarar ta fara da yammacin ranar Asabar, inda ta ci gaba da ci har zuwa ranar Lahadi.
Gobarar ta shafi kayan abinci na kasuwar.
Tinubu ya jaddada cewa yawaitar gobara a kasuwanni na jefa ’yan kasuwa cikin matsanancin hali, don haka ya bayar da umarnin a gudanar da bincike domin gano musabbabin da kuma hana sake aukuwar gobarar.
Shugaban kasuwar, Junaid Zakari, ya ce gobarar ta lalata kayayyaki da gine-gine da darajarsu ta haura Naira biliyan biyar.
Hakazalika, ya ce gobarar ta shafi ’yan kasuwa sama da 1,000, inda ya ce gobarar ta wannan karon ma daga cikin mafi munin wadda ta taɓa faruwa a tarihin kasuwar.
Ya ƙara da cewa har yanzu ba a gano inda mutum bakwai suka shiga, yayin da jami’an agajin gaggawa ke ci gaba da bincike domin gano su.