Yadda fitowar Jonathan ta sauya lissafin zaben 2027
Wannan na zuwa ne a yayin da rikicin cikin gida a PDP ya raba ta gida biyu da shari’a a kotu, inda tsagin Turaki da kuma tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, kowannensu ke sayar wa masu neman takara fom.
Ana ganin fitowar tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan takara a zaben 2027, zai kara wa abin zafi da armashi, da sauya lissafin siyasa kafin fitowarsa.
Wasu ke ganin fitowarsa za ta shafi kuri’un sauran ’yan takarar jam’iyyun adawa, musamma tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi dan takarar Jam’iyyar NDC da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar Jam’iyyar ADC da kuma da ma shi kansa Shugaban Kasa Bola Tinubu.
Tuni dai tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya samu tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2027 babu hamayya, daga tsagin Jam’iyyar PDP, karkashin jagorancin tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Kabiru Tanimu Turaki.
Tsagin Turaki, wanda ke samun goyon bayan Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince da takarar Jonathan ta hanyar dauke masa tantancewa.
Tsohon Gwamnan Jihar Neja a zamanin Jonathan, Mu’azu Babangida Aliyu, ne ya sanar da hakan a madadkin kwamitin tantacewar a zauren da tsagin nasu yake tantance sauran masu neman takara a Hotel din Transcorp Hilton da ke Abuja.
- DAGA LARABA: Abin da ya sa ’yan Najeriya suke kishin ƙabila fiye da ƙasa
- Pantami ya janye takararsa ta Gwamnan Gombe a APC
Mu’azu Babangida Aliyu ya ce jam’iyyar ta dauke wa Jonathan tantancewa ne saboda la’akari da tarihinsa na siyasa a matsayin tsohon mataimakin gwamna, tsohon gwamna, tsohon mataimkin shugaban kasa kuma tsohon shugaban kasa.
Wannan na zuwa ne a yayin da rikicin cikin gida a PDP ya raba ta gida biyu da shari’a a kotu, inda tsagin Turaki da kuma tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, kowannensu ke sayar wa masu neman takara fom.
Kowane daga cikin Turaki da Wike sun kasance ministoci a zamanin gwamnatin Jonathan, inda Wike ke matsayin Karamin Ministan Ilimi, a yayin da Turaki ke Ministan Ayyuka na musamman.
A ranar Talata ne dai PDP ta fara tantance masu neman takararta gabanin zaben 2027.
Tun bayan barin Jonathan mulki a 2015, an sha yin hasashen cewa zai fito takarar shugaban kasa, musamma a 2023, amma bai fito ba, sai wannan karo.
Wannan kuma na zuwa ne a yayin da rikicin shugabanci ya raba jam’iyyar, duk da cewa wasu na ganin zai iya dinke barakar, wadda ta yi sanadiyyar ficewar wasu manyan kusoshin jam’iyyar kamar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Gwamnan Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, wanda bai taba sauya sheka daga jam’iyyar ba.