An kammala jigilar mahajjatan Najeriya zuwa Saudiyya
Hukumar NAHCON ta ce, aikin jigilar ya fara ne a ranar 3 ga watan Mayu, sannan aka kammala shi da jirgin ƙarshe na kamfanin Max Air da ya ɗauki alhazan Jihar Zamfara daga filin jirgin saman Gusau.
Hukumar Alhazan Najeriya NAHCON ta sanar da kammala jigilar mahajjatan Najeriya zuwa ƙasar Saudiyya domin aikin Hajjin 2026.
Hukumar ta ce, aikin jigilar ya fara ne a ranar 3 ga watan Mayu, sannan aka kammala shi da jirgin ƙarshe na kamfanin Max Air da ya ɗauki alhazan Jihar Zamfara daga filin jirgin saman Gusau.
- Marasa tunani ke zaton ina yi wa Tinubu aiki — Kwankwaso
- Abin da zan sa a gaba wa’adi na biyu — Tinubu
A cewar NAHCON, an gudanar da jimillar jirage 98 cikin kwanaki 18, inda aka riƙa yin kusan jirage biyar a kullum.
Najeriya ta samu guraben alhazai 50,000 a bana, ciki har da masu yawon buɗe ido masu lasisi da jami’an gudanarwa.
Hukumar ta ce, kusan alhazai 39,000 daga ɓangaren gwamnati ne aka yi nasarar jigilar su zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji.
Sai dai ta bayyana cewa, wasu maniyyata ba su samu damar tafiya ba sakamakon rasuwa da matsalolin rashin lafiya bayan an fitar musu da biza.
Shugaban hukumar, Ismail Abba Yusuf ya yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen nasarar aikin jigilar alhazan.
Hukumar ta kuma ce, ana ci gaba da shirye-shiryen dawo da alhazai gida, wanda ake sa ran zai fara daga ranar 3 ga watan Yuni.