An kashe mutum 2 da sace wasu da shanu a Sakkwato

Majiyoyi daga yankin sun shaida cewa, maharan sun shiga ƙauyen ne da ƙafa, inda suka ajiye babura a nesa.

An kashe mutum 2 da sace wasu da shanu a Sakkwato

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe mutum biyu tare da sace mutum 17, sannan suka kwashe kimanin shanu 50 a wani hari da suka kai ƙauyen Garin Faji da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato.

Majiyoyi daga yankin sun shaida cewa, maharan sun shiga ƙauyen ne da ƙafa, inda suka ajiye babura a nesa domin kauce wa jin ƙararsu.

Wani mazaunin ƙauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, maharan sun fara harbe-harbe ba kakkautawa a lokacin da suka isa ƙauyen, lamarin da ya sa mutane suka tsere domin tsira da rayukansu.

Ya ce, harin ya yi sanadin mutuwar wani mutum mai suna Haruna Dan Kwambo da ’yarsa mai shekara takwas, yayin da aka sace matansa biyu da kuma wasu mata da yara daga cikin iyalansu.

Mazauna yankin sun ce, jimillar mutanen da aka sace sun kai 17, ciki har da maza uku, yayin da sauran mata da yara ne. Sun kuma ce an kwashe kusan shanu 50 a yayin harin.

Sun bayyana cewa, wannan ba shi ne karo na farko da ake kai irin wannan hari a yankin ba, inda suka bayyana yadda aka taɓa kai irin waɗannan hare-haren a baya da suka jawo asarar rayuka da sace mutane.

Inda suka tuno da wani hari da ya gabata da wasu mazauna ƙauyen suka nutse a jirgin ruwa a yayin da suke ƙoƙarin tserewa daga harin da aka kai masu wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar kusan mutane 10.

Majiyar ta ce, maharan sun kwashe kusan awa guda suna aikata ta’asa kafin jami’an tsaro su iso, amma a lokacin sun riga sun tsere.

Mazauna yankin sun koka da rashin isassun jami’an tsaro, tare da kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su gaggauta ceto waɗanda aka sace masu.

Duk koƙarin da muka yi domin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Ahmad Rufai, ya citura domin bai amsa kira kuma bai maido amsar saƙon da aka aike masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.