An kashe uwa da ’ya’yanta uku a Benuwe

Mazauna yankin sun bayyana cewa, iyalin suna barci ne lokacin da maharan suka far musu a gidansu.

An kashe uwa da ’ya’yanta uku a Benuwe

An bayar da rahoton kisan wasu mutane huɗu na iyali guda a wani sabon hari da wasu mahara suka kai cikin tsakar dare a yankin Imande da ke ƙaramar hukumar Guma a Jihar Benuwe.

Wakilinmu ya samu  bayanan cewa, waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da wata mata da ‘ya’yanta maza guda uku, waɗanda aka yi zargin harbe su har lahira da misalin ƙarfe 2 na dare ranar Talata a unguwar Imande Dem da ke kan titin Gbajimba a gundumar Uvir.

Mazauna yankin sun bayyana cewa, iyalin suna barci ne lokacin da maharan suka far musu a gidansu. Sun kuma ƙara da cewa, dama can mahaifin iyalin ya taɓa mutuwa a irin wannan hari da aka kai ƙauyen a baya.

Wani shaida, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa akwai wani matashi guda ɗaya da ake kyautata zaton shi ne kaɗai ya tsira a gidan, wanda ya samu raunukan harbin bindiga kuma a halin yanzu ana yi masa tiyata domin cire harsasai daga jikinsa.

Shugaban ƙaramar hukumar Guma, Orwough Maurice bai samu damar yin bayani kan lamarin ba saboda wayarsa ba ta shiga ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Ita kuwa Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta rundunar ’yan sandan jihar (PPRO), DSP Udeme Edet, ta ce har yanzu ba ta sami irin wannan rahoto ba, amma ta yi alkawarin tuntubar wakilinmu da zarar ta samu cikakkun bayanai.