Katsina za ta yi wa mutum 2,000 auren gata

Idan komai ya tafi daidai, za a gudanar da auren gatan na farko a Jihar Katsina a ranar 25 ga Afrilu, 2026.

Katsina za ta yi wa mutum 2,000 auren gata

Gwamnatin Katsina ta kammala shirye-shiryen gudanar da auren gata na farko ga amare da angwaye 2,000 da aka zakulo daga kananan hukumomi 34 na jihar.

Kwamishiniyar Harkokin Mata ta Jihar Katsina, Hajiya Aisha Aminu Malumfashi, ta ce idan komai ya tafi daidai, za a gudanar da auren gatan na farko a Jihar Katsina a ranar 25 ga Afrilu, 2026.

A yayin wani taron horaswa kan rayuwa da kuma shawarwari da aka shirya wa masu cin gajiyar shirin, Shugabar Gidauniyar Tallfin Aure ta Al’usra, Malama Murja Ibrahim Duwan, ta bayyana cewa horon na nufin bai wa sabbin ma’auratan da aka tantance ilimi da kwarewa da kuma muhimman dabaru da za su taimaka wajen samun nasarar rayuwar aure.

Ta kara da cewa za a ba su takardun shaidar kammala samun horo a matsayin sharadin shiga auren gatan.

Shi ma Darakta-Janar na Hukumar Hisbah ta Katsina, Dakta Aminu Usman Abu-Ammar, ya ce shirin auren gatan na daga cikin matakan gwamnati na rage yawaitar munanan dabi’u a cikin al’umma.

Ya bayyana cewa akwai mata zawarawa, marayu da kuma masu rauni da ke son yin aure amma rashin karfin tattalin arziki ya hana su. Ya ce shirin zai bai wa amaren tallafi, haka kuma an tanadi kayan tallafi ga kowane ango domin saukaka rayuwarsu.

A nata jawabin, Kwamishiniyar Harkokin Mata ta Jihar Katsina, Hajiya Aisha Aminu Malumfashi, ta bayyana cewa dukkan sabbin ma’auratan su 2,000 sun riga sun yi gwaje-gwajen lafiya da tantancewar dacewa kafin auren.

Sai dai ba a bayyana adadin kudin da aka ware domin shirin ba tukuna.