Babu Shugaban da ya taimaki Arewa kamar Tinubu — Uba Sani

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi wata tawagar fadar shugaban ƙasa da ke rangadi a yankin Arewa maso Yamma.

Babu Shugaban da ya taimaki Arewa kamar Tinubu — Uba Sani

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya bayyana cewa babu wani shugaban Najeriya da ya taimaka wa Arewa kamar Bola Ahmed Tinubu cikin shekaru ƙalilan da ya yi a mulki.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi wata tawagar fadar shugaban ƙasa da ke rangadi a yankin Arewa maso Yamma.

A cewarsa, matakan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka sun taimaka wajen rage matsalar tsaro a jihar Kaduna tare da inganta muhimman ayyukan more rayuwa.

Ya ce, a lokutan baya tafiya daga Kaduna zuwa Birnin Gwari na ɗaukar lokaci mai tsawo saboda matsalar tsaro, amma yanzu an samu sauƙi, tare da qaruwar zirga-zirga da kuma bunƙasar kasuwanci.

Gwamnan ya ƙara da cewa, waɗannan sauye-sauye sun jawo farin jini ga shugaban ƙasa, inda ya yi hasashen cewa hakan zai taimaka masa a zaɓen 2027.

Sai dai wasu shugabannin Arewa sun bayyana ra’ayi dabam, suna zargin cewa, ana nuna rashin daidaito wajen rabon ayyuka da manufofin gwamnati tsakanin Arewa da Kudanci.

Shugaban kwamitin amintattu na Qungiyar ACF, Bashir Dalhatu ya ce mutane da dama a Arewa na da ra’ayi mai gauraya kan yadda gwamnatin ke tafiya.