Boko Haram ta kashe Janar din soja a Borno
Birgediya Janar O. O. Braimah, wanda shi ne Kwamandan Rundunar Soji da ke Benisheikh ya gamu da ajalinsa ne bayan harin da kungiyar ta kai a cikin tsakar dare.
Wani babban soja mai mukamin Janar ya mutu bayan harin da wasu mahara da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne suka kai a Karamar Hukumar Kaga ta Jihar Borno.
Birgediya Janar O. O. Braimah, wanda shi ne Kwamandan Rundunar Soji da ke Benisheikh ya gamu da ajalinsa ne bayan harin da kungiyar ta kai a cikin tsakar dare.
Shaidu sun bayyan cewa maharan sun kuma hallaka fararen hula da mambobin jami’an tsaron sa-kai na Sibiliyan JTF da da jami’an tsaro da mayakan Boko Haran na daga cikin wadanda suka mutu a arangamar a garin Benisheikh da kuma yankin Pulka da ke Karamar Hukumar Pulka.
’Yan ta’addan Boko Haram sun kai mummunan hari a garin Benisheikh da misalin karfe 1 na dare a ranar Alhamis, inda suka kona manyan motoci da lalata motocin kasuwanci.
- Rikicin Shugabancin Jam’iyyar ADC ya kara kamari
- Mutum 2000 sun bar garuruwansu sakamakon janye jami’an tsaro a Zamfara
Rahotanni sun ce direbobi da fasinjoji da ke kan hanya sun yi kwanan dole a garin saboda rufe hanyar Maiduguri–Damaturu da ake yi a kowace yamma.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa kwamandan sojojin, Birgediya Janar Braimah, ya rasa ransa a yayin arangamar. Wani mazaunin garin, Malam Lawal Benisheikh, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, “Innalillahi wa Inna’ilaihin raji’un. Boko Haram sun sake kashe kwamandan sojojin Benisheikh. Allah Ya jikansu.”
An ce sojoji sun yi nasarar kashe da dama daga cikin ’yan ta’addan, sai dai wasu jami’an tsaro sun rasa rayukansu, ciki har da kwamandan, yayin da ’yan ta’addan suka kwashe motocin soja.
Majiyoyi sun kara da cewa kafin kai harin Benisheikh, ’yan ta’addan sun fara kai hari a Pulka da Bakin Ruwa da ke karamar hukumar Gwoza da misalin karfe 10:30 na dare, inda suka mamaye sansanin soja, suka kona kayan aiki da motocin yaki.
Mayakan Boko Haram sun kuma kwashe kayan abinci daga shaguna a Pulka tare da lalata injina da kayan aikin kamfanin gina hanya. Pulka dai na dauke da dubban ’yan gudun hijira daga Ngoshe, bayan garin ya fuskanci hari a watan da ya gabata.
Hedikwatar Operation HADIN KAI (OPHK) ba ta fitar da sanarwa kan harin ba a halin yanzu.