Rikicin Shugabancin Jam’iyyar ADC ya kara kamari
Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’yyar, Nafiu Bala Gombe ne ya jagoranci zanga-zangar, tare da dan Majalisar Wakilai daga Jihar Kogi, Leke Abejide, da daruruwan magoya bayansu.
Rikicin shugabancin Jam’iyyar ADC ya kara tsananta a ranar Alhamis, bayan wani tsagi na jam’iyyar karkashin jagorancin Nafiu Gombe ya gudanar da zanga-zanga a hedikwatar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ke Abuja, inda suka bukaci a ba su sahalewar doka.
Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’yyar, Nafiu Bala Gombe ne ya jagoranci zanga-zangar, tare da dan Majalisar Wakilai daga Jihar Kogi, Leke Abejide, da daruruwan magoya bayansu.
Masu zanga-zangar sun zargi bangaren tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark, da yunkurin kwace shugabancin jam’iyyar ba bisa ka’ida ba.
A yayin da yake jawabi ga jami’an INEC, Nafiu Gombe ya ce dole ne a bi tsarin doka wajen warware rikicin shugabanci. Ya ce, “Ba za ka shigo ADC ta taga ba ka ce kana son kifar da masu jam’iyyar. ADC jam’iyya ce ta ’yan Najeriya daga matakin unguwanni har zuwa kasa.”
- Katsina za ta yi wa mutum 2,000 auren gata
- Har yanzu akwai matsalar hauhawar farashi a Najeriya — Bankin Duniya
Shi ma Honorabul Abejide ya yi kira ga INEC da ta ki yarda da abin da ya kira yunkurin kwace jam’iyyar, yana mai jaddada cewa kundin tsarin mulkin ADC ya fayyace sharuddan cancantar shugabanci.
Ya ce dole ne mutum ya shafe akalla shekaru biyu a jam’iyyar kafin ya iya neman mukami.
A nasa bangaren, Daraktan Matasa na ADC, Mohammed Sahad, ya yaba wa INEC bisa bin umarnin kotu, amma ya bukaci hukumar ta tabbatar da Nafiu Gombe a matsayin shugaban jam’iyyar na gaskiya.
Da yake mayar da martani, Kwamishinan INEC na Kasa, Abdullahi Abdu Zuru, ya tabbatar wa masu zanga-zangar cewa hukumar za ta duba korafinsu kuma ta ba su amsa.
Zanga-zangar ta zo ne washegarin da jagorancin David Mark, ya gudanar da gagarumar zanga-zanga a Abuja karkashin taken #OccupyINEC, inda suka zargi hukumar da take hakkin dimokuradiyya da tsarin shugabanci na cikin gida.
Wannan jerin zanga-zangar ya nuna yadda rikicin shugabanci ke kara zurfi a jam’iyyar ADC, lamarin da ke haifar da damuwa kan makomar jam’iyyar a gaba.