Dan Majalisa ya fashe da kuka yana rokon a sake zaben shi

Ɗan majalisar, wanda ya shafe shekaru 16 yana rike da wannan kujera, ya fashe da kuka ne a lokacin da yake roƙon shugabannin mazabarsa da ke neman sabon wakili.

Dan Majalisa ya fashe da kuka yana rokon a sake zaben shi

Honorabul Audu Mustapha Ganga

Honorabul Audu Mustapha Ganga, mai Wakitar Mazabar Magumeri a Majalisar Dokokin Jihar Borno, ya fashe da kuka, yana roƙon al’ummar mazabar su sake zabensa a karo na biyar.

Ɗan majalisar, wanda ya shafe shekaru 16 yana rike da wannan kujera, ya fashe da kuka ne a lokacin da yake roƙon shugabannin mazabarsa da ke neman sabon wakili.

A wani bidiyo da ya bazu, ya ce: “Kun san daga talakawa na fito, amma na yi muku abubuwa da dama. Ina yi muku alƙawarin wakilci mafi kyau idan aka ba ni wata dama.”

Majiyoyi sun bayyana cewa zuwa yanzu akalla mutane shida ne suka riga suka sayi fom ɗin neman takarar kujerar ta Mazabar Magumeri.

Sai dai roƙon da ya yi cikin kuka ya jawo ce-ce-ku-ce a kafofin sada zumunta.

Abubakar Hassan ya ce: “Yanzu ka tuna cewa ka fito daga gidan talakawa bayan ka raina shugabanninka, ka san gwamna ba zai bar ka ba.”

Mu’azu Hassan ya ce: “Ba sauƙi ba ne samar da abinci ga iyali. Babu abinci ga rago.”

Lawan Modu ya ce: “Hon. Ganga ya yi tasiri ga rayuwar matasa da mata ta hanyar ƙarfafa su da samar da ayyukan yi. Yin kuka ba alamar rauni ba ne.”

Muhammad Abba Kura ya ce: “Kukan da kake yi na munafirci ne.”

Lamarin ya ci gaba da jawo muhawara tsakanin masu goyon baya da masu adawa da shi, yayin da ake jiran yadda za a kaya a zaben fid-da-gwani na mazabar Magumeri.