DSS ta kwace fasfon El-Rufai
DSS ta kaddamar da bincike kan sace Abubakar Dadiyata a zamanin mulkin El-Rufai a Kaduna
A safiyar Litinin din nan Hukumar Tsaro ta Kaya (DSS) ta kwace takardar fasfo na tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
A ranar ce dai El-Rufai ya gabatar da kansa a Hedikwatar Hukumar Yaki da masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) da ke Abuja, domin amsa tambayoyi.
Hukumar ta kuma sake bude bincike kan bacewar fitaccen mai suka ga gwamnatin El-Rufai, Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, wanda wasu da ba a sani ba suka dauke shi da karfi a gidansa da ke Kaduna a zamanin mulkin El-Rufai a shekarar 2019.
Majiyoyi masu tushe a DSS sun shaida wa Aminiya cewa hukumar ta fara binciken bacewar mutane da dama a Kaduna da ake alakanta da tsohon gwamnan.
Dadiyata, malami a Sashen Turanci da Harsuna na Jami’ar Tarayya Dutsinma, Katsina, ya bace ne a ranar 1 ga watan Agusta, 2019, bayan wasu da ba a san su ba sun sace shi daga gidansa a Kaduna. Har yanzu ba a san inda yake ba.
- DSS za ta binciki El-Rufai kan zargin odar guba —ONSA
- Dalilin da Kasuwar Singa take yawan yin gobara
- Yau El-Rufai zai bayyana a ofishin EFCC
An sake kira da a binciki bacewarsa a makon da ya gabata, bayan jami’an tsaro sun yi yunkurin kama El-Rufai da zarar ya dawo daga kasar Masar.
A wata hira da gidan talabijin na ARISE El-Rufai ya ce ya samu labarin cewa wani dan sanda ya taba ikirarin cewa shi da wasu daga Kano ne aka turo domin su sace Dadiyata.
Sai dai ya jaddada cewa ba shi da masaniya kan rayuwar Dadiyata, wanda ya ce mai goyon bayan tafiyar Kwankwasiyya ne, kuma abokin adawar tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.
A cewar El-Rufai: “Ba ni da wata alaka da shi. Matsalarsa Ganduje ce. Idan akwai wanda za a tambaya kan bacewarsa, to gwamnatin Kano ce, ba ta Kaduna ba.”
Sai dai wani babban jami’i a hedikwatar DSS ya bayyana cewa an kwace fasfon El-Rufai ne don hana shi komawa Masar bayan dawowarsa na dan lokaci. Ya kara da cewa har ’ya’yan tsohon gwamnan suna cikin wadanda ake bincike kan bacewar Dadiyata.
Majiyar ta ce: “El-Rufai ya san ana binciken sa kan bacewar Dadiyata. Shi ya sa ya yi shirin ziyartar EFCC da ICPC kafin ya koma birnin Alkahira. Amma kwace fasfon ya dagula shirin nasa.”
Jami’in ce binciken da aka sake budewa ya nuna cewa El-Rufai na da hannu a sace Dadiyata, duk da cewa yana kokarin jingina lamarin ga Ganduje da wani dan sanda da ba a tabbatar da shi ba.
Ya ce: “Bacewar Dadiyata ta jawo hankalin duniya, har ma kungiyoyin kare hakkin bil’adama irin su Amnesty International suka shiga. Amma duk da haka, El-Rufai bai taba mika wannan muhimmin bayani ga hukumomin tsaro ba.”
A cewar jami’in, El-Rufai da ’ya’yansa biyu suna fuskantar bincike kan lamarin, kuma kwace fasfon nasa na da matukar tasiri ga makomar tafiyarsa.