Gobarar Singa: Shettima zai jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa Kano
Tinubu ya yi alƙawarin tallafa wa ‘yan kasuwar.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Mataimakinsa Kashim Shettima, da ya jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa Jihar Kano a ranar Litinin, domin jajanta wa waɗanda gobarar kasuwar Singa ta shafa.
’Yan kasuwa da dama sun yi asarar kayayyaki na biliyoyin Naira a gobarar da ta tashi a ƙarshen mako, wadda ita ce ta biyu cikin makonni biyu da ta auku a kasuwar.
- Gobarar Singa: Tinubu ya jajanta wa ’yan kasuwar Kano
- Adawar siyasa ta fara daidaita a Kano — Gwamna Abba
Tawagar za ta isar da saƙon jaje na shugaban ƙasa tare da tabbatar wa ’yan kasuwar Gwamnatin Tarayya za ta tallafa musu.
Haka kuma za su yi aiki tare da Gwamnatin Jihar Kano domin gyara kasuwar cikin gaggawa.
Daga cikin waɗanda za su kai ziyarar akwai Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau I. Jibrin, Ministan Harkokin Jin-ƙai Bernard M. Doro, da Babbar Daraktar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) Zubaida Umar.
Shugaba Tinubu ya kuma yi waya da Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf domin jajanta wa ’yan kasuwar da al’ummar jihar.
Gobarar ta fara tashi ne da yammacin Asabar kuma ta ci gaba da ci har zuwa yammacin ranar Lahadi, inda ta lalata kayayyakin abinci masu yawan gaske.
Shugaban ya kuma bayar da umarnin a gudanar da bincike kan yawaitar tashin gobarar a kasuwar.