Gwamnan Bauchi na neman sabuwar jam’iyya bayan tattaunawarsa da APC ta rushe

Burga ya ce za su ci gaba da tattaunawa domin nemo jam’iyyar da ta dace da mutanensu.

Gwamnan Bauchi na neman sabuwar jam’iyya bayan tattaunawarsa da APC ta rushe

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya fara neman jam’iyyar da zai koma bayan tattaunawarsa da jam’iyyar APC ba ta kai ga cimma matsaya ba.

Shugaban jam’iyyar PDP mai biyayya ga tsagin Tanimu Turaki a Jihar Bauchi, Samaila Adamu Burga ne, ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Asabar.

Ya ce jam’iyyar APC ba ta aminta da karɓar buƙatun gwamnan ba.

A cewarsa, shugabannin APC sun fara tattaunawa da Gwamna Bala Mohammed ta hannun Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Farfesa Yiltwada Netanwe, da kuma Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya kai ziyara Bauchi domin lallashinsa ya koma APC.

Sai dai tattaunawar ta rushe ne saboda APC ba ta amince da tsarin rabon muƙamai na kashi 60 da 40 da aka gabatar domin tafiyar da jam’iyyar a Bauchi ba.

Burga, ya bayyana cewa a wasu jihohin da gwamnoni suka koma APC, irin wannan tsari an amince da shi.

Ya ce ba zai yiwu gwamnati ta kawo cikakken tsarinta daga matakin mazaɓa har zuwa jiha ba tare da samun cikakken iko a jam’iyyar ba.

Ya kuma bayyana cewa Gwamna Bala Mohammed ne, ke jagorantar tattaunawar tun daga farko.

Bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki na PDP da kuma nazari mai zurfi, jam’iyyar ta yanke shawarar dakatar da tattaunawar.

Burga, ya ce yanzu suna duba yiwuwar ƙulla alaƙa da wasu jam’iyyun siyasa kafin yanke hukunci na ƙarshe.

Ya bayyana ƙarara cewa  ƙofarsu a buɗe take ga sauran jam’iyyun siyasa domin tattaunawa, amma ban da APC.

Ya ce PDP a Bauchi tare da gwamnan da sauran manyan masu ruwa da tsaki na duba hanyoyin siyasa mafi dacewa da za su kare muradun al’ummar Jihar.

Ya ƙara da cewa duk da cewa har yanzu ba su zaɓi sabuwar jam’iyya ba, tabbas za su koma inda mutanensu za su samu kwanciyar hankali da damar tsayawa takara a zaɓuka.