Iran na shirin dakatar da shirinta na nukiliya
Amurka ta yi watsi da wannan tayin, inda ta nace cewa dakatarwar ya kamata ta kai akalla shekaru 20, domin tabbatar da cewa Iran ba za ta ci gaba da shirinta na nukiliya ba a nan gaba
Iran ta bayyana cewa tana iya dakatar da shirinta na nukiliya na tsawon shekara biyar, a wani yunkuri na rage tashin hankali da kuma buɗe ƙofar tattaunawa da Amurka.
Rahotanni sun nuna cewa wannan tayin na daga cikin koarin diflomasiyya da ake yi domin dakile rikicin da ya dade yana kara kamari tsakanin ƙasashen biyu, musamman kan batun sarrafa makamashin nukiliya.
Sai dai gwamnatin Amurka ta yi watsi da wannan tayin, inda ta nace cewa dakatarwar ya kamata ta kai akalla shekaru 20, domin tabbatar da cewa Iran ba za ta ci gaba da shirinta na nukiliya ba a nan gaba.
Wannan sabanin ra’ayi ya nuna yadda ake ci gaba da takaddama tsakanin ɓangarorin biyu, duk da ƙoƙarin da ake yi na samar da matsaya ta hanyar sulhu.
- An kama mutum 33 da ake zargi da hannu a harin cocin Kwara
- NAJERIYA A YAU: Abun Da Ya Sa Matan Arewa Ke Gujewa Karantar Ilimin Kimiyya
A halin yanzu, ana sa ran za a fara wani sabon zagaye na tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a ranar Alhamis, inda ake fatan za a samu wata mafita kan batun.
Masu sa ido kan harkokin duniya sun ce nasarar tattaunawar na da muhimmanci wajen rage tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, musamman a daidai lokacin da ake fama da rikice-rikice da suka shafi tsaro da makamashi.