Makinde ya fito takarar Shugaban Najeriya a Jam’iyyar APM
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani babban gangamin haɗakar jam’iyyun PDP da APM da aka gudanar a dandalin Mapo Hall da ke garin Ibadan, babban birnin jihar, Ibadan.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya bayyana aniyarsa a hukumance ta tsayawa takarar shugabancin ƙasa a zaɓen shekarar 2027.
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani babban gangamin haɗakar jam’iyyun PDP da APM da aka gudanar a dandalin Mapo Hall da ke garin Ibadan, babban birnin jihar, Ibadan.
- ’Yan bindiga sun sace Basarake a Katsina
- Kwamishinan El-Rufai ya shiga takarar Gwamna a Jam’iyyar ADC
Makinde ya sanar da wannan ƙawance ne ƙarƙashin wani yunƙuri da ya kira “Reset Nigeria Moɓement” (Yunkurin Sake Fasalin Najeriya).
Gwamnan ya bayyana cewa:“Saboda da haka, a yau, ni Oluseyi Abiodun Makinde, FNSE, ina sanar da takarara ta neman mƙamin Shugaban Najeriya.”
Ya bayyana cewa wannan ƙawance ya biyo bayan zargin wani ƙullalliya na son ƙaƙaba tsarin mulki na jam’iyya ɗaya kacal a Najeriya.
Makinde ya jaddada cewa, lokaci ya yi da za a sake fasalin Najeriya ta hanyar tunkarar ƙalubalen tattalin arziki, zamantakewa da siyasa da ƙasar ke fuskanta.
“Wannan ne lokacin da za mu fuskanci fargabarmu. Kada ku ji tsoro,” in ji Makinde, yayin da yake kira ga ’yan Najeriya da su shiga cikin al’amuran ci gaban ƙasa a matsayin ’yan ƙasa ba wai a matsayin ’yan kallo ba.