Masarautun Kano sun dakatar da Hawan Sallah

An danganta matakin da umarnin da hukumomin tsaro suka bayar bayan shirinsu na gudanar da hawan sallah.

Masarautun Kano sun dakatar da Hawan Sallah

Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a lokacin hawan Juma’a

Sarakuna biyu da ke iƙirarin kujerar sarautar Kano, wato Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero, sun sanar da dakatar da dukkan haye-hayen Babbar Sallah da aka shirya gudanarwa a jihar.

Sanarwar ta fito ne daban-daban daga ɓangarorin biyu, inda suka danganta matakin da matsalolin tsaro da kuma umarnin da hukumomin tsaro suka bayar bayan shirinsu na gudanar da hawan sallah.

Tun farko dai, kowanne ɓangare ya sanar da aniyarsa ta gudanar da hawan a lokacin bikin Babbar Sallah, lamarin da ya janyo damuwa a tsakanin al’umma kan yiwuwar samun rikici tsakanin magoya bayansu.

Da yake jawabi a madadin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, Matawallen Kano, Alhaji Aliyu Ibrahim, ya ce majalisar masarautar ta samu bayanan tsaro da ke nuna yiwuwar wasu ɓata-gari za su yi amfani da hawan wajen haddasa tarzoma da tayar da hankalin jama’a.

Ya ce an ɗauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya da kuma kiyaye doka da oda a lokacin bukukuwan sallah.

Haka nan, Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Dan’agundi, ya sanar da dakatarwar a madadin Aminu Ado Bayero, yana mai cewa sun amince da umarnin ’yan sanda domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

A ranar Laraba dai, ɓangarorin biyu sun gudanar da hawan sallah a wurare da hanyoyi mabambanta, kafin daga bisani su dakatar da sauran bukukuwan hawan.

Rikicin Masarautar Kano ya samo asali ne tun bayan mayar da Muhammadu Sanusi II kan karagar mulki da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a 2024, bayan tuɓe Aminu Ado Bayero daga sarauta — shekaru huɗu bayan tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sauke Sanusi a 2020.

Tun daga lokacin ne rikicin yake ci gaba da ɗaukan hankali a gaban kotuna daban-daban, lamarin da ya janyo dakatar da ɗaya daga cikin fitattun al’adun Hausawa na hawan sallah a Kano a shekarun baya bayan nan.