NAJERIYA A YAU: Abin da dokar kasa ta ce kan takarar Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya yi duba ne kan tanadin dokar kasa kan kace-nace da ake yi kan takarar shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Siyasar Najeriya ya sake ɗaukar hankali yayin da jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tsohon Shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, zai tsaya mata takarar shugaban ƙasa a zaben 2027.
Wannan batu ya tayar da muhawara a tsakanin masana, da ’yan siyasa da ma al’umma.
Idan za a iya tunawa dai, an rantsar da tsohon shugaban ƙasan, har sau biyu: a karo na farko a shekarar 2010 bayan rasuwar tsohon Shugaban Kasa Umaru Musa Yar’adua, sannan kuma a karo na biyu a 2011 bayan lashe zaben da ya biyo baya.
Amma abun tambayar a nan shi ne, shin ko me dokar kasa ta bayyana kan takarar tsohon shugaban kasan bayan rantsar da shi har sau biyu kan kujerar shugaban kasa?
Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
- NAJERIYA A YAU: Halin da matan da aka yi garkuwa da suke ciki
- DAGA LARABA: Abin da ya sa ’yan Najeriya suke kishin ƙabila fiye da ƙasa
Domin sauke shirin, latsa nan