NLC ta ’yantar da matashiyar da ta haihu a gidan yari

Ƙungiyar ta shawarci alƙalai da suke sassautawa masu ƙananun laifuka.

NLC ta ’yantar da matashiyar da ta haihu a gidan yari

Ƙungiyar Ƙwadago ta Mata (NLC) reshen Jihar Jigawa, ta taimaka wajen sakin wata matashiya mai shekaru 22 da ke shayar da jariri a gidan gyaran hali na Garki, bayan biya mata tarar da kotu ta yanka mata.

Shugabar ƙungiyar, Kwamared Salma Ilyasu Abubakar, ta bayyana haka yayin da take magana kan ayyukan alheri da suka gudanar a bikin Ranar Mata ta Duniya ta shekarar 2026.

Ta ce sun gano matar ne lokacin da suka kai ziyara gidan gyaran halin domin rabon tallafi, inda suka tarar da ita ɗauke da jariri ɗan watanni biyu.

“Mun bincika, sai muka gano cewa an tsare ta ne saboda ta kasa biyan tarar kotu, kuma tana cikin gidan gyaran halin ne ta haifi jaririn,” in ji ta.

Ta ce daga nan suka tura lauyansu domin ya bi diddigin shari’ar, har aka samu nasarar sakinta bayan sun biya tarar.

Shugabar ta nuna damuwa kan halin da gidajen gyaran hali ke ciki, tana mai cewa akwai buƙatar gwamnati da ƙungiyoyi su haɗa kai domin gyara matsalolin.

Ta kuma ce sun fahimci cewa mutane da yawa na tsare ne saboda ƙananan matsaloli da za a iya warware su ba tare da tsare su ba.

Haka kuma, ta roƙi alƙalai da su riƙa la’akari da halin mata masu juna biyu da masu ƙananan laifuffuka, maimakon tura su gidan gyaran hali.

Ta yi alƙawarin cewa ƙungiyar za ta ci gaba da kai ziyara da taimaka waɗanda suke cikin irin wannan hali.