Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin
Sojojin sun sanar da tsige Shugaban Kasa Patrice Talon da kuma rushe duk hukumomin kasar.
Sojoji a kasar Jamhuriyar Benin sun sanar da hambarar da gwamnati a wani yunkurin juyin mulki a ranar Lahadi.
Sojojin sun bayyana ne a gidan talabijin na kasar inda suka sanar da tsige Shugaban Kasa Patrice Talon da kuma rushe duk hukumomin gwamnatin kasar.
Kamfanin Dillancin Labaran kasar Faransa (AFP) ya ruwaito cewa an ji karar harbi a kusa da Fadar Shugaban Kasar.
Dakarun, karkashin jagorancin Laftanar-Kanar Pascal Tigiri, sun rufe iyakokin kasar da rushe jam’iyyun siyasa.
- Dalilin da ya sa ’yan sanda suka kama ni — Muhuyi
- Jirgin sojin sama ya yi hatsari a Neja
- Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno
Zuwa lokacin kammala wannan labarin babu cikakken bayanin halin da Shugaba Talon masi shekara 67, wanda ke kan karagar mulkin tun a 2016 yake ciki.
Amma ministan harkokin kasar, Olusegun Ajadi Bakari, ya ce an samu yunkurin kifar da gwamnati, amma sojoji na neman shawo kan lamarin.
Ofishin Shugaban Kasar ya sanar cewa Shugaba Talon yana cikin koshin lafiiya, kuma sojojin kasar na kokarin murkushe wasu ‘yan tsiraru da ke yunkurin juyin mulkin.