Sufeto-Janar na ’yan sanda ya ba da umarnin tsaurara tsaro a makarantun Katsina
Rundunar ta shawarci jama’a da suke sanya ido a makarantu game da motsin mutane.
Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Disu, ya bayar da umarni a ƙara tsaurara tsaro a makarantu a Jihar Katsina domin kare ɗalibai da malamai daga hare-haren ’yan ta’adda.
An bayyana wannan umarni ne ta bakin Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda mai kula da harkokin kuɗi da mulki, Sulaiman Abdul, yayin ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar.
- Wata mata da yara 2 sun tsere daga hannun ’yan ta’adda a Borno
- Yadda aka sayar da jariri sabon haihuwa N2.5m a Legas — ’Yan Sanda
Ya ce an umarci ’yan sanda a Katsina da su ƙara sintiri, inganta sa ido, tattara bayanan sirri, da kuma tabbatar da kasancewar jami’an tsaro a makarantu.
A cewarsa, wannan mataki na nufin daƙile hare-hare, inganta saurin kai ɗauki cikin gaggawa, da kuma tabbatar da tsaro a makarantu.
A yayin ziyarar, tawagar ’yan sandan ta ziyarci wasu makarantu, ciki har da Makarantar Yaran ’Yan Sanda da kuma Kwalejin Fasaha da Kasuwanci ta ’Yan Mata da ke Ƙaramar Hukumar Charanchi, domin duba matakan tsaro.
Sun duba katanga, ƙofofi, wuraren tsaro da kuma yadda ake tura jami’an tsaro a makarantu.
Haka kuma, Babban Jami’in ya gana da shugabannin makarantu domin tattauna matsalolin tsaro da hanyoyin inganta kariya.
Ya shawarci makarantu da su ƙara tsaurara tsarin shigar mutane, su kasance cikin sanya ido, tare da gaggauta kai rahoton duk wani abu da ake da shakku ga hukumomin tsaro.
Rundunar ta jaddada cewa tana ci gaba da ƙoƙari wajen kare makarantu da tabbatar da cewa ɗalibai da malamai na karatu cikin aminci.