Tarayyar Turai ta ci tarar Temu dala miliyan 232

Wannan ne karo na biyu da EU ke cin wani babban kamfanin intanet tara ƙarƙashin dokar Digital Services Act (DSA).

Tarayyar Turai ta ci tarar Temu dala miliyan 232

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ci kamfanin kasuwancin intanet na Temu tarar Yuro miliyan 200 — kwatankwacin dala miliyan 232, bisa zargin sa da gaza hana sayar da haramtattun kayayyaki masu haɗari a ƙasashen Turai.

Matakin ya biyo bayan wani bincike na tsawon shekaru biyu da aka gudanar bayan hukumomin kare haƙƙin masu sayen kaya daga ƙasashen Turai 17 sun gabatar da ƙorafe-ƙorafe kan ayyukan kamfanin.

Hukumomin EU sun ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa masu amfani da dandalin a Turai na iya cin karo da kayayyaki masu haɗari kamar kayan wasan yara masu ɗauke da sinadarai masu illa da kuma cajar wayoyi marasa inganci.

Ƙungiyar ta ce Temu ya gaza tantancewa da nazartar haɗarin da irin waɗannan kayayyaki ke haifarwa ga masu amfani da shi a ƙasashen Turai.

Kamfanin Temu, wanda ya fara aiki a kasuwar Turai a shekarar 2023 kuma yanzu yake da abokan hulɗa sama da miliyan 130 a EU, ya ce bai amince da hukuncin ba, yana mai bayyana tarar a matsayin wacce ta wuce kima.

Kwamishiniyar fasaha ta EU, Henna Virkkunen ta ce girman kasuwar Temu a Turai na nufin cewa miliyoyin mutane na iya samun irin waɗannan haramtattun kayayyaki cikin sauƙi.

Wannan ne karo na biyu da EU ke cin wani babban kamfanin intanet tara ƙarƙashin dokar Digital Services Act (DSA), bayan da aka ci dandalin X tarar Yuro miliyan 120 a watan Disambar bara.

A ƙarƙashin dokar DSA, manyan dandalan intanet da suka haɗa da kafafen sada zumunta da kasuwancin yanar gizo wajibi ne su tantance haɗurran da ayyukansu ke haifarwa tare da ɗaukar matakan kariya.

EU ta bai wa Temu wa’adin zuwa ranar 28 ga watan Agusta domin ya gabatar da shirin yadda zai magance matsalolin da aka gano, ko kuma ya fuskanci ƙarin hukunci.

Har ila yau, EU na ci gaba da binciken wasu zarge-zarge kan Temu, ciki har da amfani da wasu dabaru da ake zargin na jefa masu amfani cikin ɗabi’ar dogaro da dandalin.