Ya mutu bayan fada da dan shekara 12 a Yobe

Ana ci gaba da kokarin kama dan shekara 12 da ake zargi da kisan, da kuma hakikanin abin da ya faru

Ya mutu bayan fada da dan shekara 12 a Yobe

Wani matashi dan kimanin shekara 14, Musa Umar, ya mutu bayan wata mummunar hatsaniya da ta hada shi da wani makwabcinsu mai shekara 12 a kauyen Jama’are da ke Karamar Hukumar Fika a Jihar Yobe.

Majiyoyin tsaro sun ce lamarin ya faru ne a ranar 30 ga Afrilu, 2026, da misalin karfe 10:00 na dare lokacin da wata takaddama ta hada Umar Musa fada da wani karamin yaro, mai shekaru 12, wanda ya buga wa Musa sanda a kai.

Majiyoyin sun bayyana cewa an fara garzayawa da Musa asibitin garin Gadaka don neman magani kafin daga bisani a tura shi  zuwaBabban Asibitin Fika saboda tsanantar yanayinsa.

A cewar majiyar, bayan an kai Musa asibitin da aka tura su, likita ya tabbatar da cewa ya riga ya rasu kafin a karaso da shi.

Rahoton ya kara da cewa daga bisani bayan dogon binciken an mika gawarsa ga iyayens don a yi mata jana’isa bisa tsarin addinin Musulunci.

Majiyoyin sun kuma ce ana ci gaba da kokarin kama dan shekara 12 wanda ake zargin, da kuma hakikanin lamarin.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar ta Yobe SP Dungus Abdulkareem ya tabbatar da faruwar lamarin duk da cewar har yanzu lamarin bai kawo gare su ba, amma dai suna da labarin hakan.