NAJERIYA A YAU: Yadda Raguwar Maniyyatan Najeriya Ke Shafar Aikin Hajji

Ko ta wadanne irin hanyoyi ne raguwar maniyyatan Najeriya ke tasiri ga sauke farali? Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

NAJERIYA A YAU: Yadda Raguwar Maniyyatan Najeriya Ke Shafar Aikin Hajji

A ’yan shekarun nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa sauke farali da kuma masu hidimta musu.

A shekarun baya Najeriya na samun kujerun aikin Hajji sama da dubu casa’in daga gwamnatin ƙasar Saudiyya, amma cikin ’yan shekarun da suka gabata adadin yana ta raguwa zuwa kusan dubu sittin da biyar.

Ko yaya ƙara raguwar kujerun maniyyatan Najeriya ke yin tasiri ga ƙasar?

Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai yi duba a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan

Amurka za ta sayar wa Saudiyya makaman dala biliyan 1.96

Majalisar Ukraine ta amince da sabuwar gwamnati

Salihu Lukman ya fice daga Jam’iyyar ADC

Kotu ta hana FRSC tare motoci a titunan Kano