’Yan bindigar da suka sace matafiya 6 na neman fansar N100m a Benuwe
Huɗu daga cikin waɗanda aka sace mambobi ne na ƙungiyar Ansaarudeen, waɗanda suka taso daga Ilorin a ranar Litinin.
Wasu ’yan bindiga sun sace matafiya shida a safiyar Talata a kusa da ƙauyen Kula da ke kan hanyar Naka–Makurdi a Ƙaramar Hukumar Gwer West ta Jihar Benuwe.
Majiyarmu ta ruwaito cewa bayan kusan awa biyu da sace mutanen, maharan sun kira iyalansu suna neman kuɗin fansa har Naira miliyan 100.
Shaidu sun bayyana cewa mutanen da abin ya shafa, maza uku da mata uku, na tafiya ne a cikin wani ayarin motoci lokacin da ’yan bindigar suka tare su da asubahin Talata, suka yi awon gaba da su.
Bayanai sun ce huɗu daga cikin waɗanda aka sace mambobi ne na ƙungiyar Ansaarudeen, waɗanda suka taso daga Ilorin a ranar Litinin, suka isa Naka da dare.
Rahotanni sun nuna cewa sun sauka sun kwana, sannan da misalin ƙarfe 5 na asuba suka sake ɗaukar hanya, inda suka yi arba da maharan da suka yi awon gaba da su.
Sai dai wasu majiyoyi sun ce mutanen sun kwana ne a yankin Ankpa na Jihar Kogi kafin su taso da asubahin Talata zuwa Makurdi, amma aka tare su a ƙauyen Kula da ke kusa da Makurdi.
Ɗaya daga cikin mazajen matan da aka sace ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa maharan sun tuntubi iyalai jim kaɗan bayan harin suna neman Naira miliyan 100.
“Su shida ne — maza uku da mata uku. Yanzu haka ana ta ƙoƙarin ganin yadda za a samo kuɗin,” in ji shi.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwer West, Victor Ormin, shi ma ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Makurdi, inda ya ce matafiya ne aka kai wa hari yayin da suke tafiya cikin ayari.
“Gaskiya ne, na tabbatar da sacewar. An shaida min sun bar Naka da misalin ƙarfe 5 na asuba kafin su faɗa hannun ’yan bindiga da suka sace wasu daga cikinsu,” in ji Ormin.
Ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne a kusa da Makurdi a kan hanyar Naka–Makurdi, amma bai tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba a lokacin da yake magana.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benue, DSP Udeme Edet, bai amsa kiran waya ko saƙonnin da aka aika masa domin jin ta bakinsa ba.
Wannan lamarin dai ya sake jefa fargaba a zukatan matafiya da mazauna yankin, musamman ganin yadda hanyar Naka–Makurdi ta zama tamkar komar ’yan bindiga a ’yan kwanakin nan.