’Yan sanda sun ceto mutum 5 daga hannun ’yan bindiga a Zamfara

Jami’an sun tafka ƙazamin artabu da maharan kafin samun nasarar ceto mutanen.

’Yan sanda sun ceto mutum 5 daga hannun ’yan bindiga a Zamfara

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, ta samu nasarar ceto mutum biyar da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a kan hanyar Anka zuwa Bukuyum.

Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindigar sun tare matafiyan biyar a hanya suka tafi da su cikin daji.

Bayan samun bayanan sirri, ’yan sanda suka bi sahunsu har zuwa maɓoyarsu.

Nan take aka yi musayar wuta tsakanin ’yan sanda da ’yan bindigar.

Daga bisani ’yan bindigar suka gane cewa jami’an tsaro sun fi su ƙarfinsu sai suka tsere suka bar mutanen da suka sace.

Jami’an sun samu nasarar kuɓutar da dukkanin mutanen biyar ba tare da sun samu rauni ba.

Haka kuma sun ƙwato babura biyu da ’yan bindigar ke amfani da su.

Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce rundunar na ci gaba da yaƙi da ’yan ta’adda domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Ya kuma buƙaci jama’a da su riƙa bayar da haɗin kai da kuma sanar da jami’an tsaro duk wani abu da ba su gamsu da shi ba cikin gaggawa.