’Yan sanda sun ceto yaran da ’yan bindiga suka sace a Zamfara
Rundunar ta ce za ta ci gaba da farautar ragowar maharan da suka tsere domin fuskantar hukunci.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, ta ceto ’ya’yan malamin Kwalejin Fasaha ta Ƙaura Namoda, su uku da ’yan bindiga suka sace.
Kakakin rundunar, DSP Yazid, ya ce bayan samun rahoton aukuwar lamarin suka samar da rundunar haɗin guiwa, inda suka bi bayan ’yan ta’addan.
- Rikicin Shugabanci: ADC ta kori Nafiu Bala da wasu 10 daga jam’iyyar
- Dikko Radda ya jagoranci taro kan matsalar ’yan daba a Katsina
“Hakan ya kai ga samun nasarar ceto ’ya’yan malamin su uku da aka sace. Yanzu haka suna tare da iyalinsu.
“Muna ci gaba da bibiyar ’yan bindigar da suka tsere domin ƙwato sauran mutum guda da ke hannunsu.
A wani labarin mai kama da wannan, wasu da ake zargin ’yan bindiga ne, sun kai wa ’yan sandan sintiri da ke Gundumar Mada a Gusau hari.
DSP Yazid, ya ce rundunar samu nasarar kama mutum biyu daga ciki, yayin da sauran suka tsere da raunuka.
Rundunar ta tabbatar wa al’umma cewa za ta ci gaba da aiki domin kamo ’yan ta’addan da suka tsere tare da tarwatsa sauran da suka addabi jihar.